Mobiles Phones

Gyaran Waya-Yadda Ake Unlocking Na Keypad Phone 2023

Koyon Gyaran Waya A Saukake Dalla Dalla 2023

Yadda Zaka Koyi Gyaran Waya Dalla-Dalla 2023

Mobile Softrepair wannan wata hanya ce da ake bi wurin warware matsalan wayoyin hannu ta hanyar amfani da nau’rar Computer wanda mafi akasari irin wannan gyaran shine yafi kawo kudi sosai a harkan gayaran waya saboda zaka iya kirawa mutum kudin da kake so kuma ya biyaka anan take musamman idan yana tsoron kai wayar cikin birni.

Wannan hanya da SOFTREPAIR zaka iya gudanar da ita a ko ina kake a fadin duniya sannan kuma bata bukatar network abunda ake bukata shine ka tabbata cewa computer ka ka saita mata komai idan nace komai ina nufin kayan aikin sune drivers da kuma tool da zakayi wannan aikin dashi wanda zamuyi bayaninsa anan gaba kadan.

SHAWARA:
Duk abunda zakayi ka tabbata ka maida hankali sosai wurin gudanar da flashin na waya sannan ka tabbata kana haddace hanyar da kabi wurin unlocking na kowacce waya saboda kuwa idan aka kawo maka irinta gobe kada kasha wahala sosai.
Sannan ka tabbata kana taka tsantsan da masu kawo maka flashing saboda kuwa idan kowa ya kawo kana karba kawai to tabbas watarana zaka tsinti kanka a gidan yari.
Ka rike wannan a matsayin sana’a hakan zai taimaka maka sosai wurin ci gaba da bincike da warware matsalan jama’a.

Tsarin Security Na Kananan Waya One Click Unlock Any Phone

A wannan gabar zamuyi bayani gameda yadda tsarin secuirty na kananan wayoyi suke da yadda suke aiki, munada kananan wayoyi kala kala sannan wadannan wayoyi da kuke ganinsu sunada babbanci halittarsu dakuma siffar jikin su dakuma sunayensu.
  • SPD
  • MTK
  • Qualcomm
MTK yana nufin Mediatek: a karkashin wannan model din akoi wayoyi masu yewan gaskiya sannan mafi yewanci wayoyin da muke aiki dasu MTK phones ne, bari muga misalan mtk phones.
Misalan MTK Phones:
  • Techno
  • Infinix
  • Gionee
SPD Yana nufin Spreadtrum: Shima wannan akoi wasu adadin models na wayoyinda muke amfani dasu a karkashinsa wanda wadannan wayoyi sun hada da mafi yewan london use da muke aiki dasu bari muga misalan su:
Misalan SPD Phones:
  • Itel
  • Lenovo
  • ZTE

Qualcomm:Wannan shima wani nau’in model ne wanda akoisu daga cikin wayoyin da muke amfani dasu sannan shima tools nashi yana nan a yelwace.

Misalan Qualcomm Phones:
  • Samsung
  • Xiaomi
  • ZTE

Wadannan sune karkasuwan wayoyi wanda mukafi aiki dasu sannan sanin wannan zai baka damar warware matsalan waya idan aka kawo maka shi.

Yadda Ake Saita One Click Unlock Any Phone Tool

Drivers Installation
Yanzu bari muyi saitin Computer namu ta zama Ready wato zamu saita mata kayan flashing a kanta amma wadannan tools na kananan wayoyi zamuyi aiki dashi anan.
Matakin farko shine kayi downloading na wadannan drivers din duka:
Bayan ka kammala downloading sai kabi wadannan matakan kamar haka idan kana amfani ne da windows 8, 10, 11/masu 64bits to dole sai kayi Disable na driver signature naka saboda ya baka damart installing na unsign driver domin yin disabled na driver signatur naka sai kabi wannan matakan:
bayan ka kammala sai kayi install na wannan drivers din ta hanyar bin wannan guide din shima kamar haka:
Tools Installation:
A wannan mataki zamu nuna maka tools da ya kamata kayi amfani dashi wurin gudanar da unlocking a kananan wayoyi (keypad phone) wanda wadannan tools din zasu taimake ka sosai sannan kuma guarantee ne basuda wata matsala.
Da farko kayi downloading na wadannan tools din guda biyu
Cire Security Na Ko Wace Karamar Waya One Click Unlock

Wadanna sune tools guda biyu wanda zasu taimaka maka wurin cire security na kowace karamar waya cikin kankanin lokaci.

Miracle Thunder Wannan tool din yana amfani sosai kusan gaba daya wadannan keypad model din yana Repairing nasu sannan kuma yanada CPU masu yewa acikinsa both SPD MTK Qualcomm. sannan miracle box yana ayyuka da dama bayan cire secuirty wanda idan kuna biye damu acikin wannan shafin namu zaku koyi abubuwa da yewa.
Yadda ake amfani da miracle thunder wurin cire security na karamar waya

Wannan hoton yana dauke da duk abunda kakeson sani gameda cire security na karamin waya ga bayani dalla dalla:

  1. Bayan ka bude miracle thunder naka sai ka duba idan wayar da zaka mata flashin wace iri ce amma mafi yewanci MTK ne wayoyin hannun mu sai kuma SPD wato su Itel phones.
  2. Daga nan saika zabi FORMAT
  3. Saika zabi Auto yana nan ta gefen dama na boot select.
  4. Saika Danna START BUTTON
  5. Saika samu USB Cable mai kyau kayi connecting na wayar dashi daga nan ka jirata saita nuna maka DONE.

MTK Flashtool Wanna n kuma yana supporting na MTK phones ne kadai Wanda yana cire security cikin second 3 zuwa 5 kachal sannan yanada saukin aiki sannan kuma wannan zaka iya sakashi a cikin flash naka ko wani lokaci zaka iya budeshi domin kuwa shi baya bukatar installation.

Yadda ake amfani da MTK Flashtool wurin cire security na karamar waya

Bayan ka sauke wannan tool din na MTK Flashtool kawai saika bude shi zakaga setup file din sunanshi ya kare da .EXE bayan ka danna akansa zai bude maka kamar haka.

  1. Saika tabbata yana kan Read back saika zabi format
  2. Sannan saika dannan OK 
  3. Sai ka Connecting na wayar ka da USB Cable 
  4. Daga nan ka jira second 3 zuwa 5 shikenan zai nuna maka good da green color shikenan.

Wadannan sune a takaice tools da hanyar da zaku bi wurin unlocking na kananan wayoyi SPD, MTK, da Qualcomm sannan zaku iya tambayar abunda baku gane ba zamu kara muku bayani ko kuma ku tuntubemu a shafukan mu na facebook da whatsapp 08129986028.
muna godiya sosai.

Leave a Reply

Back to top button