Health Tips 2023

Sahihin Maganin Mura Na Gargajiya Hadi Mai Kyau

yadda zaku magance matsalar mura da yoyon hanci

Sahihin Maganin Mura Na Gargajiya Sha Yanzu Magani Yanzu

Mura wata cuta ce da take addabar jama’a musamman lokacin sanyi da lokacin hazo ana fama da cutan mura sosai da sosai wanda zaka ga har likitoci ma suna fama dashi wannan ya sanya jinyar mura yake da matukar wahala zaka rika shan magani amma har yanzu kaga taki fita.

To insha Allah a yau na kawo muku magani hadin gargajiya wannan hadin an jarrabashi yana magani sosai sannan babu cutarwa ko kadan acikinsa .

Ga masu fama da matsalar mura ko sarkewar makoshi ko toshewar makoshi ko dai wata lalura a makoshin ko murya ta kasa fita yadda ake bukata sakamakon mura ko tari ko dai wata cutar dabam.

A samu wadan nan abubuwan kamar haka:

  • Citta
  • Kurkum
  • Lemon tsami
  • Sassaken Marke ( Danye ko sabon diba, ba wanda ya dade a ajiye ba)
  • Zuma

Yadda Ake Hada Maganin Mura Na Gargajiya

Sai a tafasa Citta, Lemon tsami ( har bawon), Sassaken Marke da Kurkum, idan sun tafasa sai a tace a sanya zuma daidai gwargwado sai a rika shan kofi daya da safe, da rana ma a tafasa sai a sha, da daddare ma a kara tafasawa a sha har sai lalaurar ta tafi cikin Hikimar ALLAH.

Insha ALLAH wannan hadin bugu da kari yana karawa garkuwar jiki karfi, yana tacewa mutum jini daga kwayoyin cututtuka, kuma ya kashe duk wata ƙwayar cutar da take kawo matsalolin makoshi da gabobin mutum.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button