Yadda Ake Maganin Sugar Da Jar Kabewa Gargajiya
Yadda Ake Maganin Sugar Da Jar Kabewa
Ka samo Kabewa nunanniya sai ka yanka ta a tsaye ka dauki kamar mai nauyin grm 100 sai ka bare bawon ka sanyata a cikin blender sai ka zuba ruwa dan kadan sai ka markadeta.
Bayan ka markadeta sai ka tace ka rika sha da safe kafin kayi breakfast (bude baki) da mintuna 20, kayi haka har tsawon wata daya.
Yin hakan yana magance:
- Tunbi
- Kitse
- Yana rage Sinadarin Cholesterol a jikin mutum.
- Yana tace Sugar da take cikin jini.
- Yana wanke Qoda kuma ya magance matsalar Urea.
Da sauran matsalolin jini..
KARIN BAYANI
Ka fin kafara amfani da maganin yana da kyau kafara zuwa asibiti a gwada jininka sannan bayan ka kammala shan na wata daya ma kaje asibiti a auna jininka, In Sha ALLAHu za kayi mamakin yadda jikinka zaiyi kyau sosai cikin iko da Yardar Allah.
Wanda yayi amfani da maganin na tsawon wata daya zaiga fitsarinsa ya sauya saboda zai rika fitar da wadan nan matsalolin ne ta hanyar yin fitsari da Yardar Allah.
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.
Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.