Health Tips 2023

Sahihin Maganin Lariyan Hannu-Sha Yanzu Magani Yanzu 2023

Ingantaccen Maganin Lariyan Hannu

Ko kanada wannan matsala ta lariyan hannu wanda jama a ke yewan ambaton ta, toh insha Allah yau nazo muku da ingantaccen  Maganin Lariyan Hannu wanda wannan magani mun jarrabashi mun tabbatar akoi waraka sosai acikinshi.

Sannan kuma wannan magani bai sabawa shariya ba wato magani ne zaka yishi bisa kan hanya ba tare da ka kauce hanya ba, abunda ake bukata shine ka tabbata ka tsarkake niya kafin ka aiwatar da wannan magani saboda kuwa Allah ubangiji shi kadai ne mai azurtawa saidai yana sanya sababi ga ko wacce irin kaddara.

Abubuwan Dake Ciki:

  • Menene Lariyan Hannu
  • Ire-Iren Lariyan Hannu
  • Yadda Ake Gane Lariyan Hannu
  • Yadda Ake Magance Lariyan Hannu

Menene Lariyan Hannu

A wannan gabar zanyi cikakken bayani gameda menene wannan lariyan hannun saboda wannan zai taimaka wadanda basu fahimci abun ba su fahimci abun ba.
Lariyan Hannu wani abu ne wanda yakan bayyana ga dan adam a lokacin da dan adam yake hada hadan kudade wanda kuwa, zai gane hakan ne a lokacin da dan adam ya fahimci cewa kudi basu zama a hannunsa daga wannan lokacin mutum zai fara nazarin menene ya sanya kudi basu zama a hannunsa.

Wato idan ka fahimci cewa kana samun kudi amma kuma kudin basu zama a hannunka to tabbas kana fama da lariyan hannu wani lokacin za a baka ajiyar kudi amma kuma saika gagara ajiye kudin sannan bazaka san lokacin da kudi zasu watse ba.

Karanta: Asirin Samun Kudi Nan Take A Yanar Gizo 2023

so da yewa mutane masu Lariyan hannu sukan shiga cikin kuncin rayuwa saboda yadda kudi yake salwanta a hannunsu ba tare da sunyi sutura ko baiwa wani ba haka kawai kudin zasu watse a hannun mutum.

Ire-Iren Lariyan Hannu

Wato Lariyan hannu ya kasu kashi biyu wadannan kasusuwan ko wanne yana amsa sunansa bisa ga aikin sa saboda kuwa wasu yadda suka dauki lariyan hannun, ba haka yake ba saboda kuwa lariyan hannun akan samu mutum mai arziki ma da ita.

  • Lariyan hannu mai watsar da kudi
  • Lariyan hannu mai lalata abubuwa

Lariyan hannu mai watsar da kudi: Wannan shine lariyan hannu wanda koda ka dade kana asusu a gida to ranar da ka dauko kudinka zakayi aiki dashi da zaran ka rike kudin nan a hannunka shikenan bazasuyi wani amfani ba sun salwanta kenan har abada wannan lariyan hannu yanada hatsari saboda koda ace ba kudinka bane muddin suka shigi hannunka to tabbas zaka iya watsar dasu cikin kankanin lokaci saboda wannan lariyan hannun tana tafiya ne da zugar shaidan duk abunda ke hannunka saika rika gani kamar naka ne karshenta sai kaje ka kashe wannan kudin ko kuma ka sayi wani abu kai kanaga kamar zaka amfana ko yalwata wannan kudin amma kuma bakasan cewa kana batawa kanka lokaci bane zakazo ka rasa wannan kudin.

 

Lariyan hannu mai lalata abubuwa: Wannan shine babba sannan mafi hatsari saboda wannan lariyan hannun zai iya hadaka da jama a sannan ya janyo maka zagi da zargi cikin mutane wannan lariyan hannun ba kudi ba koda ace motor ce wannan lariyan hannun bai bari ba zaka iya aiki a karkashin gomna ammam idan baka maida hankali ba ko sisis bazaka tsira dashi ba saboda kuwa wannan lariyan hannun duk abunda ka taba kawai abun zai salwanta.

Yadda Ake Gane Lariyan Hannu

Akoi wasu alamu da zaka gane cewa kanada lariyan hannu wanda a wannan matakin zan zaiyano su domin ka lura idan kana dashi saika dauki mataki da wuri tun kafin abun yafi karfi saboda haka sai a lura da wannan alamomi.

Na farko ci bayan kasuwanci Idan kai dan kasuwa ne saika lura da cewa kasuwancinka yana komawa baya baya, zaka sayo abu wannan makon, mako mai zuwa kuma sai kaga kudin hannunka bazasu kara saya maka irin wannan kayan ba.

Na biyu kuma shine watsewar kudi Wannan shine yafi bayyana ga jama’a daga lokacinda ka lura cewa idan kudi ya shigo hannunka baka iya jurewa saika kashe wannan kudi toh tabbas kasan cewa kanada lariyan hannu.

Na uku shine Watsewar kadara Wannan ya kunshi lalacewa na duk abunda ya kasance naka ne idan ka sayi hatsi ko dabbobi da niyyar kiwo tabbas idan kanada lariyan hannu wannan yakan watsar da wadannan kadarorin naka saboda haka lallai kana bukatar neman wannan magani na lariyan hannu domin ka magance wannan matsalar taka.

Karanta: Asirin Samun Kudi Nan Take A Shekarar 2023

Yadda Ake Magance Lariyan Hannu

Wannan hanyar sahihiya ce wanda an tabbatar da ingancinta sannan hanya ce mai sauki bazaka kashe ko sisi ba abubuwan da ake bukata shine kabi duk wani sharadin da aka gindaya maka saboda hakan shine kawai sai tabbatar da cewa ka hadashi yadda yakamata.

idan zakayi wannan magani ka tabbata kayishi ba tare da fargaba ko tsoro ba saboda kuwa matsalarka babba ce ya kamata ka bada lokaci wurin magance ta, sannan kuma abune wanda wani bazai maka ba dole saidai kai kayi da kanka wannan ya sanya akeso kabi sharudan gaba daya bari muje kai tsaye ga matakan da ake bi wurin hada maganin lariyan hannu.

Abubuwan Da Ake Bukata:

  • Tumfafiya
  • kwarya ko Kofi ko Roba
  • Tsabtaceccen Ruwa/ Faro ko Purewater

 

  1. Da farko zaka nemi itacen tumfafiya ka TUGETA da hannunka kata ka yarda ka TONA kawai riketa zakayi ka zarota daga jijiyarta
  2. Na Biyu sai ka karye JIJIYOYIN wato iya inda suka shiga cikin KASA saika wanke su su fita pes
  3. Na Uku saika zubasu cikin KWARYA, KOFI, ROBA, saika zuba masa ruwa mai dan yewa amma basai ya cika ba.
  4. Na hudu saika dauki KWARYAN ka samu JUJI/BOLA saika kaje ka ajiye ko bayan sallar ISHA’I ko Kuma irin karfe 8 zuwa 9 na dare saika barshi ya kwana.
  5. Na biyar sai kayi sammako da ASUBA kaje ka dauko wannan karyan naka (Kada kowa ya ganka)
  6. Na Shida saika debi kadan Daga CIkin Ruwan ka ajiye a gefe, sauran kuma saika WANKE HANNAYENKA saika KA SHAFE JIKINKA (wanka) sai ka shanye wanda wanda ka debe shikenan in’sha Allah zaka fara ganin canji nan da mako daya zuwa biyu ka ci gaba da kasuwancinka wannan yana karya asirai sosai da sosai.

Wannan shine a takaice muna bukatar muji feedback naku bayan kun jarraba wannan magani na Lariyan hannu wanda insha Allah ka rabu dashi kenan.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button