Health Tips 2023

Sahihin Maganin Kasala Da Kaifin Tunani Na Gargajiya

Yadda Ake Hada Shayin Goriba Domin Magance Kasala

Yadda Ake Hada Shayin Goriba Domin Magance Kasala

Akoi masu fama da kasala wanda har yakan hana mutum fita wurin nema wani lokacin idan ka kwanta barci baka iya tashi sai kaji gabobin jikinka yana maka ciwo, to insha Allah yau zamu kawo muku wannan hadin na shayin goriba wanda zai magance muku wannan matsala dama sauran matsaloli da suke damunku na yau da kullum.

Yadda AKe Hada Shayin Goriba Da Yadda Ake Amfani Dashi

Ku nemi Aya Amma busassa mai kyau dai-dai bukata sai ka nemi garin Goriba mai kyau sai ka hade waje daya ka niƙa sai sun niƙu sosai sai ka tankaɗe ka nemi ruwan dumi dai-dai girman kofin da kuke Amfani dashi wajen shan shayi sai ka sanya cokali uku manya a ciki ka fifita da kyau sai ka Sha.
Zaku sha da safe da Kuma lokacin shiga bacci.

Maganine Mai karfi Mai dandano Mai amfani ga ilahirin gangar jiki da ruhi.

  1. Yana buda kwakwalwa.
  2. Yana narka abinci nan take idan aka sha bayan an ci abinci.
  3. Yana karawa namiji karfin mazakuta.
  4. Yana kara wa namiji yawan ruwan maniyi.
  5. Yana Kara lafiyar jima’i da sha’awa ga ma’aurata sai a zanka sha akai akai.
  6. Yana Kara energy da cire kasala a ji garau a jiki.
  7. Yan karawa macce ruwan dumi
  8. Yana karawa zuciya lafiya da karfin aiki.
  9. Yana wanke hanjin ciki da suka cushe saboda ciye ciye ba maiko da zaqi.
  10. Yana Maganin kumburin ciki da tsuwar ciki da zafin ciki da qullewar ciki.
  11. Yana samarda qwayoyin halittan haihuwa na Mata da maza.(sperm and ovum)
  12. Yana maganin rama a jiki
  13. Yana kara yawan immunity da karfin aiki.
  14. Yana yakar cutukan daji na cancers
  15. Yana maganin kurajen ciki dana cikin Baki natural vitamin C ne Mai karfi.

Anaso a rika wannan hadin kullum ana sau ayi karin kumallo dashi saboda magance matsaloli dake damun mu na yau da kullum.

Sannan insha Allah wannan magani bashi da illar komai sannan gashi da dandano gashi da kamshi.

Idan akoi mai karin bayani zai iya ajiye mana comment insha Allah muna samun lokaci mu dubashi.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button