How To

Bayani Gameda Yadda Ake Kiran Rauhani Nan Take 2023

Kiran Rauhani Nan Take

Bayani Gameda Yadda Ake Kiran Rauhani Nan Take

Wannan bayani ne gameda abunda ya shafi rauhani, a wannan rubutun nawa zanyi kokarin kawo wasu hanyoyi wanda matsafa kebi wurin kiran rauhani da kuma yadda suke aiki dashi har ya rika basu wasu bayanai wanda suke bukta domin yiwa yan adam aikin tsafi kamar yadda muka sani.

Akoi wasu abubuwa da zanyi bayani game dasu domin samun haske da fahimtar ina wannan mauduin namu ya dosa sannan kuma ta wace hanya zai taimakemu.

MENENE RAUHANI DA AKE KIRA

Rauhani wani irin nau’in shaidani ne wanda bokaye da malam tsubbu suke amfani dashi wurin gudanar da aiyukansu ga jama’a, Rauhani yana kawowa bokaye da amalaman tsubbo labarai gameda abunda mutum yakeso wanda kuwa rauhani yakanyi karya wani lokacin.

Duk wanda wanda yace maka yana Aiki da rauhani Abunda ake nufi shine yana aiki da aljani wanda kuwa nafsi ya tabbatar da yadda Aljanu suke Dauko labari a sararin samaniya suke kawo wa bokaye wanda wannan shine abunda duk wanda yake aiki da rauhani yake bukata.

Karanta: Asirin Samun Kudi Nan Take A Yanar Gizo 2023

Yadda Ake Kiran Rauhani Ayi Aiki Dashi

Akoi hanyoyin yadda ake kiran rauhani wanda zan bayyanosu a  gaba ta gaba amma saidai yanada kyau kasan cewa kafin ka kira rauhani dole sai ka kafircewa Allah ga a daya wanda kuma yanada kyau kasan cewa kana kokarin kai kanka izuwaga Kafirci ne wanda yin hakan zai iya janyo maka maka fushin Ubangiji.

Yadda ake aiki da Rauhani shine a lokacinda kasamu damar kiran kiran rauhani toh anan ne zai zai gindaya maka dokokinsa wanda idan ka Amince nan ne zai zai baka hanyar da zakabi domin kiranshi a duk lokacinda aka kawo maka aiki.

Rauhani kala kala ne wanda wannan yasa babu takamammen yadda zaka kirashi saidai hanyar da ake bi domin alakantuwa da rauhanin wanda zamuyi bayani a nan gaba kadan.

Kafin ka kira rauhani sai kabi hanya wanda zai shar’anta maka kamar haka:

  • Zakayi abunda zaka zaka sabawa Allah ta yadda zakayi ridda.
  • Sannan zaka dauki littafin da ka aminta dashi na Addininka ka wulakantashi.

Sannan zai tilasta maka ziyartan filinda ya kasance wurine na zaman Aljanu cikin dare wanda wannan fitar da zakayi cikin dare shine fita wanda idan baka tsorata ba zaka hadu da Rauhani, wanda kuma akoi abubuwanda zaka hadu dasu a hanya wanda wannan ne zai zai iya lalata maka samun haduwa da Rauhanin Aljani idan kuma ka jure shikenan anan ne zai bayyana tare da baka sharuda kamar yadda muka lissafo su a sama.

Karanta: Asirin Samun Kudi Nan Take A Shekarar 2023

Yadda Zaka Kare Kanka Daga Rauhani

Akoi hanyoyi wanda addini ya koya mana gameda yadda zamu nemi tsari daga abunda ya shafi Aljanu wanda wadannan Aljanu sun hada da:

  • Fatalwa
  • Rauhani
  • Kuruwa

Wadannan sune manyan nauin Aljanu wanda suke addaban Jama’a wanda wadannan Abubuwa ne wanda akoi su koda kuwa ace baka taba haduwa dasu ba to tabbas akoisu saboda Nafsi ya tabbatar da Haka.

Menene Fatalwa

Fatalwa wani wrin nauin aljani ne wanda kamar yadda ake ake siffantashi yakan bayyana ne bashida iyaka abunda nake nufi shine zaka daga kanka kana kallonsa bazaka ga karshensa ba.

Yadda Ake Neman Tsari Daga Fatalwa

A lokacinda Fatalwa ya bayyana gareka ko kuma kana tafiya cikin tsoron kada ka gamu da fatalwa abunda zakayi shine ka rika karanta “Suratul Kursi’u” Tare da Bismillah.

Menene Rauhani

Wannan munyi bayaninsa a Rubutu daya gabata wanda mukace wani irin nauin Aljani ne wanda bokaye keyin amfani dasu.

Yadda Ake Neman Tsari Daga Rauhani

Hanyar da zakabi wurin nesanta kanka daga Rauhani shine ka kasance baka wasa da IBADA sannan kadaina yarda da CHAMPE CHAMPE wanda wannan shine zai ba Rauhani Tasirin Kusantar ka.

Menene Kuruwa

Kuruwa wani irin aljani ne wanda ko wani mutum yana dashi wanda idan ka mutu yake bayyana da siffarka yana tsorata jama’a sai a Rika gani kamar kaine.

Yadda Aka Neman Tsari Daga Kuruwa

Shima Wannan ka kasance kana Addua Kafin Kwanta Barci ka rika karanta “Suratul Kursiu” Suratul Ikhlas, Falaqi Da Nasi, wadannan sune zasu kareka daga duk wani nau’in fatalwa.

Wannan shine a takaice hanyoyinda ake bi domin alakantuwa da Aljanu da kuma wanda akebi domin nisanta kai daga garesu.

Idan kana aiki da Aljanu dole zaka rika rika basu commission na nikinsu wanda wannan shima abune mai wahala wanda wani Aljanin ruwa kawai yakeso wani kuma Jini yakeso Jinin Dabba Kona Mutum wanda dole sai ka Rika Nema masa Wannan.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button