Koyon Cryptocurrency Cikin Sauki 2024
MENENE MAANAR CRYPTOCURRENCY
Cryptocurrency nau’i kudaden digital ne masu zaman kansu, da su ke daukar matsayin kudaden saye da sayarwa ko kuma kadarori da a ke kasuwancinsu akan internet. Bambancin cryptocurrency da kudaden digital da mu ke amfani da su shi ne: kudaden digital da mu ke amfani da su ikon samar da su da gudanar da su yana hannun Gwamnati da cibiyoyin kudade, yayin da cryptocurrency kuma ikon samar da su da gudanar da su yana karkashin ilahirin al’ummar da suka yarda da su kuma suka amince su karɓe su a matsayin kudade ko kadarorin da za a iya hada-hadarsu. Tsarin cryptocurrency da gudanarwar su yana kama da na zinare, kasancewar shi ma zinare yana daukar matsayin kudi sannan yana daukar matsayin kadara wanda a ke iya saye ko sayarwa.
ABUBUWAN DA SUKA HADA CRYPTOCUREENCY
Cryptocurrencies a matsayin kudade ko a matsayin kadarori suna da siffofi da tsarukan da su ke wanzuwa akan su. Ga su kamar haka:
- Digital Decentralised Pseudonymous
- Transparency Global
- Limited Supply
Digital: Cryptocurrency suna wanzuwa ne a siffar lambobi da za a iya turawa ko karbar su ta hanyar amfani da internet, hakan na nufin babu su a zahiri, babu kudin takardarsu ko kuma tsabobinsu. Kasancewar su digital ya sa suna da saukin dauka a je duk inda a ke so ba tare da wani ma ya san.
Akwai su ba. Ta wannan fannin za a iya cewa cryptocurrencies sun fi zinare saukin dauka da saukin ajiya domin shi zinare yana da gangar jiki kuma ana iya taɓa shi ko rike shi ba kamar cryptocurrency da ke a siffar lambobi ba.
Decentralised
Cryptocurrencies suna wanzuwa ne akan tsari mai yanci wanda babu wata hukuma ko Gwamnatin da ke da ikon kula da mu’amalolin da a ke yi da su ita kadai. Kowa na iya samar da su matukar dai al’umma sun yarda da su to za a iya mu’amala da su a matsayin kudade ko kadarori. Ta fuskar adana bayanansu ma, babu wani rumbun ajiyar bayanai na wata Gwamnati ko wata hukuma da ke adana bayanan mu’amalolin da a ke yi da su.
Pseudonymous
Cryptocurrencies suna dauke da cikakken sirrin mallaka ta yadda za ka iya turawa ko a turo maka su ba tare da sunanka ko bayananka sun fito ba. Ba kamar kudaden gargajiya ba da kafin ka iya tura su ko ajiye su a cikin asusunka dole kana bukatar bude account na banki, yayin budewar kuma sai an bukaci; cikakken sunanka, adireshinka, shekarunka, jinsinka har ma da katin shaidarka duk domin a iya gane ka a kuma iya gane mu’amalolin da ka ke yi, sannan idan za a bincike ka a iya samun bayananka cikin sauki. Su kuwa cryptocurrencies wajen amfani da su ba ka bukatar sanya bayananka sannan idan ka tura su ko kuma an turo maka ba za a taɓa iya gane cewa kai ne ka tura ko kuma kai aka turowa ba. Duk mu’amalolin da ka yi da cryptocurrencies daga kai sai Allan da ya halicce ka ne kawai ku ka sani, bayan ku babu mai sani ko da ya bincika. Idan za ka saye su za ka saye su ne ba tare da sanin wajen wanda ka saya ba, idan za ka sayar da su za ka sayar da su ne ba tare da ka san wanda ka sayarwa ba.
Transparency
Duk da an samar da cryptocurrency da cikakken tsarin ɓoye bayanan masu gudanar da mu’amaloli, amma kuma suna da sigar fayyace duk mu’amalolin da aka yi da su. Yayin gudanar da mu’amaloli da kudadenmu na gargajiya bankuna ne ke ajiye bayanan tarihin mu’amalolin da aka yi, bankunan ne kadai ke damar kallon mu’amalolin da mutane su ke yi da kudadensu. Amma cryptocurrencies kuwa, babu wata cibiya da ke adana bayanan mu’amalolin da aka yi da su, maimakon hakan bayanan na warwatse ne a kowacce computer ko wayar da a ke amfani da ita wajen yin mu’amalolin da suka shafi cryptocurrency din. Saboda haka, kowa zai iya ganin cryptocurrency din da aka tura daga wata wallet zuwa wata wallet, amma babu wanda zai iya gane wanda ya tura da wanda aka turawa. Hakan na nufin, cryptocurrency a bayyane su ke kuma a boye su ke. za a iya ganin adadin cryptocurrency din da ke cikin kowacce wallet ma, idan mai wallet din ya tura cryptocurrency zuwa wata wallet, za a ga turawar da adadin yawan cryptocurrency din da aka tura, lokacin da aka tura har ma kudin cajis din da aka caji wanda ya tura. Sai dai ba za a iya gane wanda ya tura da wanda aka turawa ba.
Global
Kamar yadda a lokacin da a ke amfani da zinare a matsayin kudi ko ina ka je a fadin duniya za ka iya cinikayya da zinare ba tare da ka bukaci yin canji ba, haka su ma cryptocurrencies a ko ina kake a fadin duniya za ka iya mu’amala da su. Saboda cryptocurrency ba kudin wata kasa ba ne ballantana ya zamanto a iya kasar kadai za ka iya kashe su, su kudin al’umma ne da za ka iya kashewa a duk inda al’umma su ke a fadin duniya matukar dai al’ummar sun yarda da su. Ba sa kuma dogaro da tattalin arzikin wata kasa ballantana idan tattalin arzikin kasar ya karye hakan ya shafi kimarsu, su suna amfani ne da tattalin arzikin kansu da kansu. Bugu da kari, kasuwancin su bai keɓanta da wata kasa kadai ba, idan kana da su za ka iya sayarwa mutumin da ke a wata kasar daban, kuma kai ma za ka iya saye daga mutumin wata kasar.
Limited Supply
Ba kamar kudadenmu na gargajiya da Gwamnati kan iya buga duk adadin da ta ke so idan ta bukaci hakan ba, kowanne cryptocurrency na zuwa ne da kayyadadden adadin (Total supply) da yawansa ba zai taɓa wuce wannan adadin ba. Misali: adadin yawan Bitcoins guda 21,000,000 ne, saboda haka har abada Bitcoin zai tabbata ne a guda 21,000,000, ba zai taɓa wuce haka ba, ba ma zai taɓa karuwa ko da da guda daya kacal ba. Kayyadadden adadi da cryptocurrencies ke zuwa da su, yana daga cikin abin da ke sanyawa su kara daraja da baiwa masu kasuwancinsu damar samun riba a kankanan lokaci. Rashin kayyade adadin kudadenmu na gargajiya na daga cikin dalilin da ke sanyawa darajarsu ke raguwa.
Da yawan mutane suna da tunanin cewa, tunda Gwamnati ce ke buga kudi to mai zai sanya Gwamnati ba za ta dinga bugawa tana rarrabawa al’umma don kawar da talauci ba? Masu irin wannan tunanin ba su fahimci cewa darajar kudi na karuwa ne idan adadin kudin ya yi karanci a hannun al’umma ba. Idan ya kasance kudade suka yi yawa a hannun mutane, bukatar kudin domin yin cinikayya ta ragu to darajar kudinma za ta ragu. Ya ka ke kallo idan ya kasance kowa ya noma masara a Nijeriya?
Idan kowa ya noma masara to tabbas bukatar sayen masara dole za ta ragu, don haka farashin masarar ma dole ya ragu. Saboda me? Saboda wa zai sayi abin da yana da wadatar sa?
To kamar haka ne idan kudade suka yi yawa a hannun al’umma, darajarsu za ta ragu gwargwado yawan da suka yi hannun al’ummar.
Yadda kayyadadden adadin cryptocurrencies ke taimaka masu wajen daga darajarsu shi ne, a lokacin da cryptocurrency ya ke sabo, mutanen da suka mallake shi za ka ga ba su da yawa sosai, saboda haka ba zai yi daraja sosai ba. Amma daga baya cryptocurrency din na samun karɓuwa adadin masu bukatarsa na karuwa, darajarsa da farashinsa ma za su dinga karuwa.
Pros and Cons of Cryptocurrency
Cryptocurrency na dauke tarin fa’idodi da waraka akan matsalolin da suka shafi Kasuwanci da mu’amalolin kudade, a wani ɓangaren kuma suna dauke da irin nasu matsalolin da amfani da su zai iya haifarwa.
Pros
- Reducing corruption
- Eliminating extreme money printing
- Giving people charge of their own money
- Cutting out the middleman
- Serving the unbanked
- Borderless Transactions
- Liquidity
Reducing Corruption
Yayin da ka ba wa wani mutum ko wasu mutane cikakken iko akan wani abu fiye da sauran mutane to ka bude kofar cin hanci da rashawa kenan. Kasancewar kudadenmu na gargajiya da mu ke amfani da su ikon samar da su, sarrafa su da kula da su yana hannun tsirarrun mutane, hakan babbar barazana ce da za ta iya haifar da cin hanci da rashawa, domin tsirarun mutanen za su iya cin karansu babu babbaka saboda fura da ludayi na hannunsu, yadda suka dama haka kowa zai sha. Amma cryptocurrencies sarrafa su, samar da su da kula da bayanan