Health Tips 2023

Yadda Ake Magance Matsalar Kurajen Fuska Na Gargajiya

yadda zaku magance kurajen Pimples

Sahihin Maganin Kurajen Fuska Na Gargajiya

Shin kana fama ko kina fama da matsalar pimple a fuska wanda yake takura maka da bata maka fuska da kuraje, wannan ana samun wasu kuraje da suke fesowa a fuskar mutum suna masa kaikayi da kuma bata masa fuska.

Wannan matsalar tafi shafar mata ko ince yan mata musamman a lokacinda suke shekarun balaga ana samun irin wannan matsala ta fesowan kuraje a fuskar ya mace.

Sannan wasu yanmata kuma fuskar su na feso kuraje ne sakamakon aiki da wasu mayuka masu karfi ko sabulu mai karfi wanda idan bai karbi jikin mace ba nan take zai sauya mata fuska.

Abubuwan Da Ake Bukata Domin Wannan Hadin

  • Zuma babban cokali 2,
  • Karamin cokali na garin ‘ya’yan Almond ( da turanci) Lauz (da larabci).
  • Karamin cokali na lemon tsami.

Yadda zakuyi amfani da wannan hadin

Sai a kwaba su a rika gogawa a fuskar, sannan sai a wanke da ruwan dumi. Insha Allahu za a ga sauyi sosai cikin hikimar Allah.

Na san ba kowa ne yasan Lauz ko Almond ba, wata itaciya ce mai yin ‘ya’ya kamar na dabino tana fitowa ne a kasashen larabawa da gabas ta tsakiya. Ana samun ‘ya’yanta da Manta a kasuwanin da ake siyar da kayan maganin Islamic.
Har yanzu fa wasu basu gama gane menene ALMOND ko LAUZ din nan bafa…..
Amma na san dai kunsan bishiyar Umbrella ko? Ai itace Almond kuma lauz din.
To yayanta sai a fasa kwallon akwai wata yar gyada a cikin kwallon, to shi ne ake amfami da shi.
Wannan sahihin magani ne hadin gargajiya wanda bashi illa ga fuska insha Allah sai an tambayeki dame kika kashe kurajen fuskarki.
 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button