Health Tips 2023
Hadin Maganin Ciwon Sugar Diabetics Na Gargajiya
Yadda Ake hada Maganin Ciwon Sugar Diabetics Na Gargajiya
Yadda Ake hada Maganin Ciwon Sugar Diabetics Na Gargajiya
Masu fama da ciwon sugar yau bnazo muku da wani hadin na gargajiya kamar yadda kuka sani wannan shafin namu na Fixclan burinmu shine kawo muku magunguna wanda ake yinsu a gargajiyance.
Idan kana fama da ciwon suga muna mai baka shawarar ka jarraba wannan hadin da zamu bayar, kafin ka jarraba wannan hadin ka fara zuwa asibiti a duba maka sugar naka yana wani mataki ne sannan kuma bayan ka jarraba saika sake komawa a sake duba maka shi insha Allah za a ga dacewa sosai.
Abubuwan Da Zaku Nema Domin Hada Maganin Ciwon Sugar (Diabetics)
- Kubewa guda 2.
- Cucumber rabi 1/2.
- Lemon tsami rabi 1/2.
- Garin Zogale cokali daya.
- Ruwa kofi daya.
Yadda Ake Hada Maganin Ciwon Sugar Diabetics
Sai a yayyanka duk abubuwan da na lissafa din nan gutsi-gutsi, sai a sanya su a blender a zuba ruwa kofi daya sai a markada su, bayan an tace sai a zuba garin zogalen cokali daya a ciki, sai a juya su sosai idan aka tabbatar ya garwayu sai a shanye.
Kullum arika yin haka idan akayi na tsawon kwana uku ko sati daya ana yi, sai a koma asibti a duba jikin, in Sha ALLAH za a ga sauyi kwarai da gaske da YARDAR ALLAH.
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.
Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.