Health Tips 2023

Amfanin Cin Dabino Da Safe Ga Lafiyar Jikin Dan Adam

Maganin Gargajiya Da Dabino

Amfanin Dabino Ga LAfiyar Jikin Dan Adam Magani Sahihi

A wannan rubutun zan lissafo muku wasu daga cikin amfanin yin karin kumallo da dabino wanda yin hakan kan haifar maka faidoji masu yewa a jikin ka sannan yana magance matsaloli sosai.

  1. Yana warware matsalar fitar fitsari cikin ikon Allah.
  2. Yana tsaftace Hanta kuma ya wanke Qoda.
  3. Yana da amfani ga masu fama da ciwon tari ko wane iri ne kuwa da sauran cutukan kirji.
  4. Yana kara jini mai kyau a jikin mutum.
  5. Yana da matukar amfani ga masu fama da ciwon baya.
  6. Idan aka daka shi akayi garinsa ana zuba cokali 2 a nono ko madara ( ta gari ko ta ruwa) ana sha, yana matukar amfani ga lafiyar ma’aurata maza da mata domin yana karfafar kowanne a cikinsu.
  7. Garinsa idan ana sha da Nono ko madara ( ta gari ko ta ruwa) safe da dare da ruwan zafi kadan yana matukar amfani na bammamaki ga masu fama da matsalar low sperm count.
  8. Yana lalata SIHIRI kowane iri ne a jikin mutum Idan har ana cin guda 7 kullum da safe kafin ayi breakfast har tsawon wata 2 ko kwanaki 60, kuma da yardar ALLAH jikin ka zai samu tsari daga kamuwa da wani nau’in sihiri, Kambun-baka ko hassada kenan har abada sai dai wani Ikon Allah.

Wadannan Kadan kenan daga cikin Faidan Dabino ga lafiyar jikin dan Adam, Sannan kuma muna masu baiwa masu fama da Shafar aljanu cewa su dage da Salatin Annabi (SAW) da karanta suratul Qursiu insha Allah zasuga sauyi sosai saboda shaidanu basu tsayawa inda ake ambaton Allah.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button