Health Tips 2023

Yadda AKe Amfani Da Ganyen Gwanda Wurin Maganin Hawan Jini

Sahihin Maganin Hawan Jini Na Gargajiya

Sahihin Maganin Hawan Jini Da Ulcer Na Gargajiya

Masu fama da cutar, Ulcer (gyambon ciki) Hawan jini ( High blood pressure) Maleria da kuma cutar rashin samun isasshen barci ta insomnia ko makamantanta, to ga mafita Insha Allah

Yadda Ake Hada Maganin Hawan Jini Da Ulcer Na Gargajiya

Za ka samo wadataccen Ganyen GWANDA ne sai ka tsaftace shi sosai, sai ka tafasa shi da ruwa daidai kima na tsawon mintuna 20.

Bayan ya kai mintuna 20 din sai ka sauke shi ka barshi ya huce kadan (Za ka iya sanya masa zuma idan kana son ganin cikakken amfaninsa) sai ka sha kofi daya da safe, da dare ma kafin ka kwnatar bacci sai ka sha kofi daya, a ranar in Sha ALLAH za ka samu damar yin bacci wadatacce kamar wani jariri cikin.

Kuma za kayi adabo da cutar Ulcer, Hawan jini da maleria sannan kuma jikinka zai kara samun lafiya.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

Da fatan za a jarraba wannan hadin sannan a bamu feedback domin kara mana kwarin guiwa wurin kawo  muku magani a gargajiyance.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button