Health Tips 2023

Riga-Kafin Cutar Sanyi Ta Hanyar Amfani Da Ganyen Raihan

Gyaran jiki ta hanyar amfani da ganyen raihan

Riga-Kafin Cutar Sanyi Ta Hanyar Amfani Da Ganyen Raihan

Ya zama wajibi ga dukkanin jinsin mace da namiji su rika nuna kulawa matuka wajan daukar matakai da shawarwari domin gujewa kamuwa da kowanne irin nau’i na ciwon Sanyi wanda akafi sani da Infection wanda yanzu yazama ruwan dare a al’ummar mu.

Abubuwan Da Ake Bukata Ku Aiwatar Dasu

Jikin mace yana da saurin daukar cutar sanyi na Infection a ko wane irin yanayin da ake iya daukar cutar sanyin, shi yasa ake son duk mace akai akai ta rika tafasa GANYEN RAIHAN ( Doddoya/ Scent Leaf) da jar kanwa yar kadan tana shan kofi daya safe da dare idan ya huce kadan kuma tana wanke gabanta da shi ko ta rika zama/tsuguno a cikinsa musamman ga masu fama da warin gaba ko zubar farin ruwa ko wani kalar ruwa na rashin lafiya daga al’aurar su ko ma dai duk wata alama ta matsalar sanyin Infection.

Za a iya kara kanunfari ga mai bukatar haka, kuma yin hakan zaifi bayar da fa’idah kwarai da gaske.

Yin amfani da wadan nan kayan hadin yana da kyau matuka ga masu fama da matsalar sanyi su rikayi akai-akai kuma idan ma lafiyarku kalau za ku iya yinsa a matsayin riga-kafi, In Sha ALLAHu duk mai yin haka za ta samu kariya daga cutar sanyin Infection ko wanne iri ne da Yardar Allah. Ba wai iya mata ne kadai za su sha ba har mazan su ma za su iya sha.

GANYEN RAIHAN da Larabci ko DODDOYA da hausa ko EFIRIN da yoruba, ba wai wani boyayyen ganye bane a kudu da arewacin kasar nan ba, ana iya samun sa a duk inda yake fitowa musamman ma yanzu Lokacin damuna ne yana yawa sosai, kuma yana da matukar kamshi sosai ko wucewa kayi ta kusa da shi za ka ji shi yana kamshi sosai balle kuma ka taba shi ko ka sunsuna shi, shiyasa turawa ke kiransa da Scent Leaf.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button