Amfanin Nonon Akuya A Jikin Dan Adam
Muna maraba da kowa sannan muna muku fatan alakiri da kokari da kukeyi wurin bibiyar wannan shafin namu na fixclan inda muke kawo muku abubuwa da suka shafi kimiya da kuma kula da lafiyarku.
Kamar yadda kukaga wannan darasin namu zamuyi muku magana ne akan amfanin nonon akuya wanda masana suka ganoshi wanda kuma insha Allah idan akayi amfani dashi za a samu alfanu sosai da sosai.
kafin mu dubi wannan amfani na nonon akuya bari mudanyi wata matashiya kamar yadda muka saba a wannan shafin namu.
Bayani Gameda Alfanun Nonon Akuya Da Yadda Yake
A wannan gabar zamuyi bayani ne a takaice gameda alfanu da kuma yadda mutane ke kallon nonon akuya ta yadda wasu daga cikin mutane har suna kyamar wannan nono na akuya ta yadda idan kacewa mutum ga nonon akuya zaiji kyama sosai da sosai.
Ga wasu alfanu guda Takwas da zaka iya samu daga nonon akuya:
- Yana dauke da ‘Potassium’ da ke kare mutum daga kamuwa da cutar shanyewar gefen jiki, kara karfin kashi, kare mutum daga kamuwa da cutar hawan jini da makamantan su.
- Yana dauke da ‘Phosphorous’ wanda ke taimakawa wajen fitar da ababen da jiki ba ya bukata kamar zufa, fitsari da bayan gida.
- Yana dauke da ‘Vitamin A’ da ke kara karfin ido.
- Yana dauke da sinadarin ‘Manganese’ da ke kara karfin kashi.
- Yana dauke da ‘Magnesium’ da ke taimakawa mutane dake fama da rashin barci.
- Yana dauke da sinadarin ‘Amino Acids’ da ke kara garkuwan jikin mutum.
- Nonon akuya na da saurin nika abinci a cikin mutum.
- Nonon akuya na dauke da sinadarin ‘Protein’ da yafi na nonon Saniya. Yana taimaka wa jiki girma yadda ya kamata musammam ga yara masu tasowa.
Wadannan sune a takaice alfanu da zaku iya samuwa daga nonon akuya wanda kuma koda ace bakajin turanci zaka fahimci cewa wadannan abubuwa ne da zasu taimaka wa lafiyar dan adam sosai.