Health Tips 2023

Yadda Ake Kula Da Al’ada Magance Rikicewar Al’ada

Yadda Mata Zasu Hada Maganin Rikicewar Al’ada Da Kansu

A wannan darasin zan muku bayanin yadda mace zata kula da al’adar ta domin gudun rikice mata wasu lokutan akan samu masu irin wannan matsalar, kuma yana wahalar da su sosai. tundaga ciwon mara, jiri da kuma

murdawan cikin wasu kuwa har kamar za su suma suke idan wannan larura ya taso masu, da dai sauransu, babban matsalar kuma ita ce idan mace tana da irin wannan matsala

na rikicewar al’ada to babu damar ta samu juna biyu.

idan lokacin al’adar ya kusa sai ki yi kokari ki hada wannan magani, idan kuma sai bayan kin fara ne kika ga wannan bayanin to kina iya haɗawa ki yi amfani da shi.

Abubuwan da za ki nema basu da wahalar samu sannan basu

da tsada.

Abubuwan Da Ake Bukata Domin Kula Da Jinin Al’ada Cikin Sauki

  • Za ki samu garin habbatussauda mai kyau din (ana sayar
  • da shi a Islamic chemist na ko’ina)
  • Sai ki nemi ingantaccen zuma madaidaici ki saya.

(Idan kina so ki gane zuma din bashi da hadi, sai ki tsoma kan ashana a cikin zuman, bayan kin ciro ashanan sai ki kyatta shi a jikin kwalinsa.

idan ya kama zuman mai kyau ne, idan kuma bai kama ba to jabu ne).

Yadda Ake Hada Maganin Jinin Al’ada

Za ki nemo ruwan zafi madaidaici a kofin shan shayi, kamar yadda ake saka Lipton.

Sai ki debo garin habbatussauda cokali

Daya ‘teaspoon’ ki zuwa a cikin ruwan zafin da kika riga kika tanada.

Sannan sai ki zuba zuman madai-daici, sannan sai ki

 

 

Sai cokali ki kada domin su hade da juna. idan ya dan huce sai ki shanye duka.

Haka za ki rika yi safiya da yamma, kamar kwana ukku a jere.

Insha’Allah wannan matsala zai rabu da ke kuma komai naki zai dawo dai-dai.

Bayan maganin matsalar rikicewar al’adar kuma zai yi maku maganin abubuwa da yawan gaske na matsalolin jiki da inganta lafiya.

 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button