Yadda Ake Amfani Da Ganyen Rogo Wurin Kara Ruwan Nono
Sahihin Maganin Kara Ruwan Nono na gargajiya
Sahihin Maganin Kara Ruwan Nono na gargajiya
Shin ina masu fama da matsalar ruwan nono insha Allah a wannan rubutun zamu nuna muku yadda zaku kara ruwan nono domin shayarwa sannan wannan maganin bashida wata illa ga mace.
Ga Yadda Zaku Hada Maganin Ruwan Nono Ta Hanyar Amfani Da Ganyen Rogo
Mai fama da matsalar karancin Jini zai tsinko ganyen ne kamar guda 10 zuwa 15, sai ya tsaftace shi ko ya markade a blender ko ya mistsikeshi yadda dai za a samu ruwa daga jikin ganyen, sai a tace ruwan a zuba masa madarar ruwa misali madarar Peak Milk gwangwani daya a juye a ciki sai a baiwa mai fama da matsalar karancin jini CIKIN IKON ALLAH za kuga jinin ya dawo cikin kankanin lokaci.
Masu matsalar ƙarancin jinin sun jarraba kuma ana ganin fa’idar hakan.
Mai fama da matsalar karancin ruwan nono ma za ta iya yin wannan hadin tana sha sau biyu a rana har na tsawon kwanaki uku. Kuma ta rika yin miyar ganyen Rogo tana ci da tuwo ko Apu (fufu) ko sakwara da makamantansu.
In Sha ALLAHu za taga abin mamaki domin cikin kananan lokaci ruwan nonon zaizo, kuma yana samar da ingantacce kuma wadataccen ruwan nono ga mai shayarwa cikin.
Kuma mai ciki ma ta rika cin miyar Ganyen Rogo yana yakar cutar ANAEMIA Wacce mai ciki ke dauke da ita.