Yadda Zaku Hada Sahihin Maganin Ciwon Kunne
Sahihin Maganin Ciwon Kunne
Shin kuna fama da ciwon kunne ko kuma kunada yan uwa wadanda suke fama da ciwon kunne idan matslar ciwon kunne ce insha Allah anzo karshe daga yau.
Yadda Zaku Hada Maganin Ciwon Kunne Da Kanku
Za’a samu gashin mutum, normal gashi na mutum wanda aka aske.
Sai a sakashi a tukunya ko a gongoni ko a wani abu wanda za’a iya dorawa a wuta,
Sai a kona wannan gashin sai ya kone qurmus ya daskare yayi baqi qirin,
Sai banbaroshi a samu man shanu kokuma man gyaɗa, amma man shanun yafi dacewa, idan kuma ba’a samuba sai a kwaɓa da man gyaɗa na asali a kwaɓashi da wannan daskaren gashin da aka qona, a kwaɓa sosai sai asaka wannan haɗin da aka kwaɓa a gindin kunne, ko ince a bakin kunne.
Mujarrabun la shakka fihi, wannan mujarrabine duk wanda yake fama da ciwon kunne indai yayi wannan aikin zai warke da izinin Allah.