Health Tips 2023

Sahihin Maganin Ulcer Da Shawara Domin Shirin Azumi

Yadda zaku magance matslar ciwon Ulcer Da Shawara

Sahihin Maganin Ulcer Da Shawara Na Gargajiya

A yau nazo muku da sahihin maganin shawara wato yellow fever da kuma wannan cuta dake hana jama’a dama yin azumi wato ulcer wanda insha Allah idan akayi amfani da wannan hadin za a ga sauyi sosai musamman yadda muke fuskantar azumin watan ramadan na wannan shekara.

Wannan magani ne na gargajiya bawai kwayoyi ne za a baka ba, wannan hadi ne zakuyi da kanku domin samun saukin shawara da ulcer da yake damunku.

Kamar yadda muka sani, ciwon shawara ‘Typhoid’ da olsa ‘Gymbon ciki’ a hausance kenan, Ulcers suna ɗaya daga cikin rashin lafiyoyin dake ciwa mutane tuwa a kwarya, Musamman a ƙasashe masu tasowa na nahiyar Afirka.

Don haka, a yau zamu bayyana muku wadansu hanyoyi na gargajiya masu mutakar taimakawa wajen yaƙi da wadannan cututtukan kamar yadda Allah ya sauwake muna.

Abubuwan da kuke bukata domin hada waannan magani:

  • Ganyen Zogale ‘Ta Makka.
  • Ganyen Albarka.
  • Madarar gari.

Bayan an tanadi wadancan abubuwan da muka ambata sai shanya wadannan ganyayyakin a cikin inuwa inda babu rana har sai sun bushe rumus.

Idan an tabbatar sun bushe, sai yi amfani da abin daka ko niƙa sai a mayar da su gari lumui.

Yadda za’a hada maganin ulcer da shawara domin amfani:

Za’a debi garin Zogale, Albarka da Madara cokali daya-daya sai a samu ruwa masu dan zafi-zafi a kada su ciki sai a sha safe kafin a cin abinci da awa 1-2 da lokacin barci. Za’a yi hakan har tsawon kwanaki bakwai.

Sannan idan akoi zuma mai kyau zaku iya hadawa dashi domin karin faidoji Allah ya bamu lafiya baki daya zaku iya ajiye mana tambayoyinku a comments section domin mu rika baku amsa.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button