Sahihin Maganin Ciwon Gabobi Da Kasala Gargajiya
Maganin Ciwon Gabobi Da Kasala Da Bawon Ayaba
A yau nazo muku da maganin kasala wanda kasala kan haifar da abubuwa da dama wanda kasala shine zai sanyaka ka gagara tashi kaji kamar an maka duka gabobinka na ciwo.
Wani lokacin haka kawai mutum gashi gari ya waye kuma amma sai ya gagara tashi wani lokacin kanason yin karatu amma kuma sai abun ya gagareka saboda jikinka na ciwo sai kawai kaji ba abunda kakeso kamar barci.
Abubuwan Da Kasala Ke Haifarwa
- Reshin Walwala
- Reshin Tashi barci da wuri
- Reshin iya karatu
- Reshin yin sallah
da sauran abubuwa da dama wanda suna faruwa ne sanadaiyar kasala
Yadda zaku hada sahihin maganin kasala da kanku
Ruwan tafasasshen bawon abarba magani ne mai ban sha’awa na yanayin domin kula da cututtukan ciwon gabobi.
Bawon abarba ya kunshi sinadarin bromelain, wani kemikal mai dauke da sinadarai masu hana zafi da kumburi wanda zai iya taimakawa wajen rage radadi da zafi da kumburin da ke da alaƙa da amosani, ko ciwon gabbai.
Ta hanyar tafasa bawon abarba, domin fitar da ruwan masu amfani, yana haifar da abin sha mai gina jiki da warkar da ciwon gaɓoɓi da sauran cututtuka.
Yin amfani da ruwan dafaffen ɓawon abarba akai-akai na iya ba da taimako ga mutanen da ke fama da ciwon amosanin gabbai, tare da samar musu da hanyoyin da za su iya kula da yanayin rashin lafiyar su.
Kawai a tafasa ɓawon abarba a tukunya na tsawon mintuna 15, sannan a bar ruwan ya huce, za’a rika shan karamin kofi biyu kowace rana.
Insha Allah idan akayi amfani da wannan za a ga sauyi sosai da sosai idan akoi abunda kake bukatar karin bayani zaku iya mana comment.