Amfanin Ganyen Ayabar Plantain Maganin Bladder Infection
Magance Matsalar Infection
Magance Matsalar Infection Ta Hanyar Amfani Da Ganyen Ayabar Plantain
Mai fama da ciwon zuciya ko hawan jini da kuma cutar nan da ake kira Prostate cancer ko mu kirata da suna Prostate enlergment wanda ita wannan cuta ce da take kama marar mutum ko mafitsarar mutum, tayadda za rika yin fitsari da kyar ba yadda yakamata ba sakamakon toshewar mafitsarar wato dai wannan cuta takan toshe maka hanyar fitsari wanda idan har mutum bai dau matakin da yakamata akanta tun farko ba za ta iya haifar masa da matsala wacce za ta fi karfin tunaninsa. Allah ya kyauta.
Yadda Ake Hada Wannan Magani Da Ganyen Ayabar Plantain
Da farko a samo ganyen Bishiyar PLANTAIN iya gwargwado busasshen wanda ya bushe a jikinta, sai a tsaftace shi kuma a tafasa shi har na tsawon mintuna Ashirin 20minutes, sai a sauke shi a sanya zuma a ciki sai a rika shan kofi daya safe da dare.
Wannan shine yadda ake amfani dashi wannan ganyen na Plantain wanda idan akayi wannan hadi sannan akayi amfani dashi insha Allah za a ga amfaninsa sosai, domin yana magance Bladder infection wanda wannan itace take janyo matsalar fitsari. da duk wani Infection da ya shafi dubura kodai mafitsara za a rabu dashi da yardan Allah
Idan mutum yana shan wannan hadin kai akai kuma yana tauna danyen ganyen PLANTAIN din, hakan yana karawa zuciya karfi da lafiya cikin iko DA YARDAR ALLAH.
Karin Bayani Gameda Ganyen Ayabar Plantain
Ganyen PLANTAIN nake nufi ba Ganyen BANANA ba, domin suna yanayi sosai ko ince ma duk kusan kalar bishiyunsu daya ne, amma za kuga ya’yan ne suke bambanta, ita BANANA yayanta kanana ne basu kai na PLANTAIN girma ba. ALLAHu A’alam.
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.
Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.