Health Tips 2023

Maganin Ulcer Hadin Gargajiya Da Ganyen Zogale

Sahihin Maganin Ulcer Da Ganyen Zogale

Sahihin Maganin Ulcer Ta Hanyar Amfani Da Ganyen Zogale Ganyen Zogale

Sanin kowa ne cewa ulcer ta kasance cuta wanda take addabar mutane da dama wasu takan hanasu aiwatarda ibada kamar dai Azumin watan Ramada.

Ulcer takan kwantar da mutum idan tayi kuronik sannan ulcer kan janyo mutum ya rika zaban abunda zaici kamar dai abu mai Barkano da Tsamiya.

Yadda Zaku Hada Maganin Ulcer Da Ganyen Zogale

Idan mutum ya samo ganyen zogale ya zuge shi kuma ya yayyanka cabbage (kabeji ), sai ya wanke su ya tsaftace su da kyau, sai ya rika taunawa yana hadiye ruwan safe kafin yaci abinci sai kuma da dare kafin kwanciya bacci.

Duk mai fama da ciwon Ulcer yarika yin haka ko da yaushe har na tsawon watanni uku in Sha ALLAH zai rabu da cutar kwata kwata daga jikinsa.

Ammafa ganyen danye ne za ayi amfani da su ba sai an dafa su ba kuma ba a sanya musu komai su kadai kawai za arika taunawa, kawai wankewa za ayi.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

Zaku iya ajiye mana shawarwari da tambayoyi insha Allah muna samun lokacin da zamu rika bibiyar korafinku.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button