Health Tips 2023

Yadda Zaku Kula Da Fatar Fuska Maganin Kyasbi Da Pimpus

Yadda Zaku Kula Da Fatar Fuska Maganin Kyasbi Da Pimpus

Fuskar dan adam na cikin babban abunda ya kamata mutum ya kula da ita saboda fuska itace ake gane mutum da ita sannan kuma fuska ita ke dauke da abubuwa masu yewa wannan ya sanya wani lokacin haka kawai sai kaga fuskar ka ta canza ta yadda mutum zai gagara gane ka, kodai a samu wasu kuraje su fito maka a fuska ko kuma fatan fuskar da kanta ta kumbura ta yadda bazaa iya bambance waye wannan ba.

Wannan ya zama maka wajibi kasan yadda zaka kula da fuskarka domin kuwa fuska itace abunda mutum ke fara kallo gareka.

Abubuwan Da Suke Lalata Fatar Fuska

Akwai abubuwa bila adadin dake lalata fatan fuska wanda sun hada da yawan shiga rana, yawan shafe-shafen man kam fani, yawan goge fuska da kaya masu karfi, yawan saka kayan kwalliya a fuska wadda hakan ke rufe kofofin shigar iska da dai sauransu. 

Insha Allahu yau a wannan shafin namu na fixclan zamu zayyano yan wasu hanyoyin da za’abi wajen kula da fatar fuska cikin sauki.

A hakikanin gaskiya wanke fuska daga lokaci zuwa lokaci yana da matukar tasiri. ba wai lallai sai za’ayi wanka ko alwala kadai ba yana da kyau ko da bacci za’a kwanta a wanke fuska sosai saboda yana saukar da zufa, datti, da dai sauran ababen da ke iya zama a kai wadda hakan ke toshe kofofin shigar iska sannan ya haifar da wasu matsaloli kamar:

  • Janyo Kyasbi a fuska
  • Janyo Maruru a fuska
  • Yana rage kyau musamman ga mace
  • Janyo Tabo da dai sauransu

Mata da dama ba su damu da yin wanka da daddare kafin su kwanta barci ba. Wata ma tun kwalliyar da ta yi da daddare ta fita hira wajen saurayinta haka za ta shigo gida ta kwanta barci ba tare da ta wanke fuskarta ko kuma ta yi wanka ba.

Haka zalika idan aka koma dayan bangare na maza wani idan yayi wanka da safe ya fita nema bayan ya dawo ga gajiya ga ansha rana sannan ya kwanta zubur kamar buhun albasa ba wanka ba hamdala. Don haka ya kamata mu canza gaba daya, mu rika wanke fuskarki mu daga lokaci zuwa lokaci domin yin hakan yana da babbar fai’da ga lafiyar jikin mu. Wasu daga cikin sun hada da:

Abubuwan Da Yakamata Kuyi Domin Kula Da Fatar Fuskarku

  1. Wanke fuska ko wanka kafin a kwanta na sanya kwanciyar hankali, yana sanya isaka ta ratsa kofofin fuska mai kyau wadda hakan ke sanya barci mai dadi.
  2. Idan mutum ya kwanta ba tare da wanke fuska ba, mayukan da ya shafa a fuskarsa na taruwa sannan a wasu lokutan suke sanya fitowar manyan kuraje, wadda sai an yi da gasken gaske kafin a rabu da su.
  3. Yana da kyau a wanke fuska da sabulun wanke fuska mai kyau, domin fuska ba ta cika kwari ba kamar sauran bangarori na ji ba.

muna fatan kun amfana da wannan rubutun namu kuma zaku kiyaye saboda samarwa da fatan fuska lafiya.

 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button