Amfanin Shayin Lemon Tsami Da Tafarnuwa A Jikin Dan Adam
Amfanin Hadin Tafarnuwa Da Lemon Tsami
Amfanin Hadin Tafarnuwa Da Lemon Tsami
Idan ka samo kwayar tafarnuwa kamar guda goma (10) ka bare bawon, kuma ka samo lemon tsami guda shida (6) ka tsaftace shi kuma ka yayyanka shi, sai ka zuba tafarnuwar da kuma lemon tsamin har da bawon a cikin ruwan zafi kamar kofi daya ko daya da rabi sai ka barsu a kan wuta har tsawon mintuna 5.
Bayan mintuna biyar din sun cika sai ka sauke shi ka tace shi kuma kabari ya huce, idan ya yi sanyi sai ka rika shan babban cokali 1 da safe kafin kaci komai.
Kadan daga cikin amfanin wannan hadin su ne kamar haka:
Yana karawa jiki garkuwa daga kamuwa da cutar Cancer ko wacce iri ce.
Yana kawar da duk wata matsala ko lalurar da take a cikin baki kuma yana kara kyautata sautin muryar mutum ta rika fita fes-fes kuma zaqwai musamman na idan yana karatun Alqur’ani.
Yana magance duk wani nau’i na cutar Allergies dake cikin jikin mutum.
yana matukar amfani ga masu fama da cutar (paralyse) barin jiki wanda cutar Stroke karama ko babba ke haifarwa.
Yana daidaitawa kuma ya tace sugar din dake cikin jinin mutum, shi yasa ake so masu fama da cutar Diabetics su rika amfani da wannan hadin kai akai.
Yana taimakawa wajan fasawa tare da kawar da tsakuwar dake cikin Qoda kuma ya warware wa mutum matsalar dake damunsa a mara.
Yana ragewa kuma yadaidaita hauhawar jini a jikin mutum
Yana rage sinadaran cholesterol da kitsen dake jikin mutum
Yana magance cutar Ulcer ta gyambon ciki kuma yana wanke dattin ciki
Yana magance matsalar duk wani nau’i na sanyin dake jikin mutum, matukar mutum yana amfani da wannan hadin to zai ga bambanci a jikinsa game da matsalar sanyin Infection.
Kuma yana taimakawa mutum wajan rage kiba da tumbi
Idan ma mutum bazai iya shan wannan hadin ba, to zai iya kara masa ruwa kadan da zuma a ciki sai yarika sha akai akai DA YARDAR ALLAH zai ga fa’ida fiye da abinda na lissafa musmaman ma masu fama da cutar Ulcer.
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.
Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.