Sahihin Maganin Gyaran Gashi Da Laushin Gashi Na Gargajiya
Yadda Ake Gyaran Gashinkai A Gargajiya
Maganin Laushin Gashi Da Kara Tsayin Gashinkai
A samo ganyen gwanda mai kyau sosai sai a wanke shi ya fita sosai, sai a zuba ruwa kadan a cikin wata roba sai a mistsike ganyen irin yadda ake mistsike ganyen shuwaka, sai a tace ruwan.
Ko kuma a kirba ganyen a cikin turmi ko wani abin kirbawa mai kyau sai a kara masa ruwa kadan a ciki, sai a tace ruwan za aga ruwan ya yi kauri, da shi za ayi amfani.
YADDA AKE AMFANI DA SHI
Za a rika zuba ruwan ganyen ne a kan gashin ana shafawa, sai a samu wani mai kamar man kwakwa ko Man ridi da na zaitun sai a rika shafawa a saman maganin, sai a rufe kan tsawon mintuna 30.
Sai a wanke kan, bayan ya bushe sai a kara shafa masa man kwakwa da na Zaitun.
In Sha ALLAHu za a ga yadda gashin zaiyi laushi sosai kuma yakara samun lafiya da YARDAR ALLAH.
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.
Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.