Sahihin Maganin Warin Hammata Na Gargajiya
Yadda Ake Hada Maganin Warin Hammata Na Gargajiya
Yadda Ake Hada Maganin Warin Hammata Na Gargajiya
Sanin kowa ne cewa da yewan alumma suna fama da wannan matsala ta warin hammata wanda ita hammata abunda ya sanya take wari saboda wurine da yake lungu sannan baya samun isasshen iska wanda wannan yake sanyawa zufa yake fita anan daga karshe kuma idan baka yawaita wanka saika rika jin hammatanka yana wari.
Sannan kuma akoi wadanda tun asali haka halittarsu take zaka samesu suna fama da wannan matsala su kuma haka aka haifesu dashi komai wanka da mutum zaiyi sai kaji Hammatar sa tana wari wannan kuma halittace.
Abubuwan Da Ake Bukata Da yadda Ake Hadawa
BAKING SODA Baking Soda na taimakawa matuka wajen saurin kawar da warin hammata nan take ga namiji ko mace, kawai zaku nemi cokali biyu na Baking Soda da kuma cokali daya na ruwan Lemon Tsami.
Zaku hade su sai ku dunga gogawa a wurin zuwa wasu yan mintuna sai ku wanke. Wannan hadi zai taimaka sosai wajen kawar da warin.
TUFFA Zaku samu Tuffa dinku sai a nikata kusamu ruwa kadan sai ku zuba a juyashi sosai sai a samu yadi ko auduga a dinga tsomawa ana sawa a Hammata a matse har zuwa mintuna 10 zuwa 15. Sai a cire ayi haka kullum za’a rabu da warin hammata.
RUWAN DANKALIN TURAWA Wannan yafi kowanne, wajen kawar da warin hammata, zaku samu katon Dankalin Turawa sai ku nikashi a Blender idan yayi saiku matse ruwan nasa a wani wuri sai ku dinga wanke Hammatar taku dashi.
Ko kuma ku samu Dankalin Turawan kuyanka sala sala saiku dinga go gawa a hammatar taku zuwa wani lokaci kadan shima hakan zaisa warin ya fita nan take.
RUWAN TUMATUR Kisamu Tumatir naki masu kyau ki jajjaga ruwan ya fita sai ki hadasu da ruwan Lemon tsami ki dinga gogawa a Hammatar har na tsawon mintuna goma shima zai kawar miki da warin hammata.