Health Tips 2023

Yadda Zaku Magance Matsalar Nonuwa Breast Cancer Daga Cuta

MENENE BREAST SELF EXAMINATION?

Wannan wata hanyace da mata ko yan’mata ke duba ko kula da lafiyar mamansu (Nono) Don gujewa kamuwa da cututtuka kamar ciwon daji na nono ( Breast cancer) dadai sauransu.

A wannan zaman da muke ciki akoi abubuwa da dama dake janyo mana cututuka kama daga abubuwan da muke ci a matsayiin abinci dakuma abubuwan da muke sanyawa kamar sutura da sauransu.

Matar dake dauke da wannan cutar babu wani alamun ciwo da zataji tashin farko! Kawai dai wani ɗan tsiro karami ko ƙullutu wanda yake jeji ne Cancerous cell zataji cikin Nononta, Wanda akarshe ka iya jawo mata babbar illah da zatasa dole acire nonuwan gaba daya inma anyi sa’a bata warwatsu ba kenan.

Kamuwa da cutar ba laifin mutum bane, ba kuma a kamuwa ta hanyar jima’i, ko yin hulda da mai cutar.

WANII LOKACI AKEYIN BREAST SELF EXAMINATION

Zanyi kokarin amsa wannan tambayar da dai dai gorgodon sanina da kuma binciken masana kiwon lafiya da daliban ilimi.

Duk macen data kai shekara 20 abinda yaisama, anason tadinga yi duk wata musamman kwana 3-5 da fara menses (Al’adarta).

MAFITA SHINE: Duk Macen data kai aƙalla shekaru 20 yana da kyau ta koyi yadda ake duba Nono (breast self exams) domin wannan wata hanya ce da Mace zata iya ita kaɗai a ɗakinta, ko wajen wanka, ko ita da Maigidanta, ta duba Mamanta a madubi ko akwai wani canji ajiki. Gudun kamuwa da wannan ciwo.

ALAMOMIN GANE WANNA CIWO (BREAST CANCER)

Ta yadda da taji wani abu daban kamar:

  • Jin ƙullutu,
  • Jin suka cikin nonuwa kamar ana tsira mata allura, ko
  • Ganin kumburin nono haka nan, ko
  • Lotsawar wani sashi “dimples a nono, ko
  • Ganin fitar ruwa-ruwa me jini ko clear alhalin bata shayarwa, ko
  • Canzawar kalar wani sashin fatar na nono yai kamar jikin lemon ɓawo ko jaja-jajaa
YADDA AKE YIN BREAST SELF EXAMINATION

Step One

Mace ta tube agaban ƙaton Madubi ta ɗora hannayenta kan kugunta, ta kallesu a natse taga ko akwai wani yanayin canji a fatar ko ƙurji, dimples ko ƙari a jiki, gami da girman su.

Step Two 

Bayan nan sai ta juya ta gefe ta sake yin haka (wato ta duba gefen dama da hagu) ta ɗaga hannun ta ta kalli har zuwa hammatarta tunda jelar nonon nan ta shiga.

Wadannan sune a takaice yadda zakiyi muna fatan zaku koyawa yan uwa mata wannan hanya ta yadda za a samu a rage wannan cikin alumma.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button