Health Tips 2023How To

Yadda Ake Maganin Aljanu Suyi Magana

Yadda zaku hada sahihin maganin Iska Da Aljanu

Da farko ana so a samo kaashin mahauta, idan mutum yaje kasuwa yaje mahauta zaiga inda ake tara kããshin tumbin dabbobi, inda ake zubar da kaashin tumbin dabbobinda ake yankawa, to sai a ebo wannan kaashin, sannan kuma a samu tsakin miyar kuka, tsakin miyar kuka ana samun shi ne idan mata sun tankaɗe miyar kuka suna barin tsakin miyar da suka tankaɗe, to wannan tsakin da ake tarawa in an gama tankaɗe miyar shi ake so, idan kuma baka samu tsakin kukar ba zaka/ zaki iya zuwa kasuwa kisiyo kuka wadda ba’a daka ba sai kazo/ kizo gida ki dakata ki tankaɗe sai ki cire tsakin kiyi amfani da shi, bayan an samu tsakin sai a haɗa shi da wannan kããshin da aka ebo a mahauta, bayan an haɗashi da kashin mahautar sai a nemo kaikayin gero , za’a iya zuwa inda ake yin sussukar gero, a chan ake samun kaikayin geron, a ebo wannan kaikayin da ake tarawa bayan an sheke gero, in an ebo shi sai azo a haɗa shi da wannan Kããshin mahautar da Tsäkin miyar kuka da aka samo, a haɗa su wuri ɗaya, ma’ana a haɗa Kããshin mahauta da Tsakin kuka da kaikayin gero wuri daya, bayan an haɗasu sai a daka su su daku, sai a samu Jan Miski a haɗa a chakuɗa shi dasu duka, sai ayi wanka a dinga hayaki da shi, ga hoton jan miskin nan a kasa zan nuna muku saboda idan kun je siyowa ba sai kun sha wahala sosai ba.

Wannan shine jan miski idan kukaje saya ku tabbata irin wannan aka baku

Duk wanda iska ya dame shi ko wadda iska ya dame ta to a haɗa mata wannan kaikin a sakata taje tayi wanka sai azo a yimata hayakinnan, koda kuwa tana ihu ne tana faɗa tana buge buge to a sakata dole sai ta dinga yin hayain, koda ace sai an rirrike ta ne arirrike ta a dinga yi mata hayakin ta karfi da yaji, to in ana yin haka Insha Allahu ta’ala zata rabu da wannan matsalar cikin gaggawa, Aljanu da kansu firgita suke yi da shiga mugun bala’i idan suka ji wannan haɗin, wannan haɗin azaba ne ga Aljanu, Insha Allah zata samu sauki iskan zai bar jikin ta har abada alfarmar Annabi Sallallahu alaihi Wa sallama.

Allah yabada sa’a.

 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button