Amfanin Kwallon Dabino A Jikin Dan Adam
Yadda Ake Amfani Da Kwallon Dabino Da Amfaninsa
Shin ka kasance kana jefar da kwallon debino idan har kana jefar da kwallon dabino to daga yau ka daina jefarwa saboda zamu kawo muku amfanin wannan kwallon na dabino. daga yau kuma zaka daina jefarwa insha Allah.
Ana yin Coffee da garin kwallon, sai a rika shan shayi da shi a matsayin MILO ko makamancinsa bal ma ya fi Milo amfani a jiki k kuma yana dauke da ingantaccen kamshi mai dadin shake.
Yadda Zaku maida Kwallon Dabino Ya Zama Gari Cikin Sauki
Za ka samo kwallayen Dabinon ne sa ka wanke su sosai da kyau, katabbarar da komai ya fita a jikinsu kuma sun wanku da kyau, sai a tsane su su bushe a tabbatar da babu wata lema a jikinsu, sai a soya su a akan kasko tsawon mintuna 15 zuwa 20 ya danganta da yawansu, sai a dauko su a sa su a grander ko kuma wani abin daka sai a dake su suyi laushi sosai.
Yanzu sun zama Coffee, sai a rika shan shi da madara domin yana da matukar amfani sosai ga masu fama da matsaloli kamar haka:
Yana magance Matsalar cutar Sugar ta Diabetics type 1 ko type 2 da YARDAR ALLAH.
Yana maganin matsalar ciwon zuciya da YARDAR ALLAH.
Yana baiwa Qoda da Hanta garkuwa da lafiya cikin YARDAR ALLAH.
Yana karawa fatar jikin mutum lafiya da YARDAR ALLAH.
Yana maganin matsalar tsinkewa ko zubar gashi da YARDAR ALLAH.
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.
Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.