Yadda Ake Daukar Ciki Da Wuri Mace Da Miji 2023
Hanyar Daukan Cikin Da Wuri Da Magani
Fixclan gidan kimiya da fasaha, wannan shafin namu mai albarka yana yiwa kowa maraba sannan muna godiya da yadda kuke bibiyarmu, burinmu kullum shine mu faranta muku rai da warware muku matsalolinku musamman abunda ya shafi kimiya da fasaha.
A yau darasin namu zaiyi duba ne akan abunda ya shafi haifuwa wato daga aure zuwa daukan ciki har haifewa, insha Allah a wannan darasin zamuyi bayani dalla dalla domin kowa ya samu wayewa gameda wannan tsarin da Allah ya shiryawa dan Adam.
ABUBUWAN DA KE CIKI:
- Yadda Ake Daukar Ciki
- Hanyoyin Samun Ciki Da Wuri
- Maganin Samun Ciki Da Wuri
Yadda Ake Daukar Ciki
Zan amsa wannan tambayar ne bisaga ilimin binciken Alqur’ani mai girma a inda Allah ubangiji yayi mana bayani dalla dalla gameda yadda mace take daukan juna biyu wanda nasan wadansunku sun sani wasu kuma basu sani ba to insha Allah wadanda basu sani ba yau zasu sani a wannan maudu’in namu.
Ciki ya kasance ginshiki ne na duk wasu maaurata wanda kuwa shine ribar aure sannan duk wani magidanci yakan shiga halin kunci da damuwa idan matarsa bata samu haifuwa ba haka suma iyayenmu mata sukan shiga cikin kunci da damuwa idan basu samu haifuwa ba wanda hakan kan janyo su shiga zuwa wurin bokaye da malamai wanda kuma idan baabi a hankali ba har a shiga sabon Allah wanda kuma daga karshe ayi biyu babu.
Yadda ake samun ciki shine hanyar saduwa tsakanin mace da miji wato wadannan jinsi biyu su suke haduwa su samar da ciki.
A yayinda mata da miji sukayi jima’i wannan maniyi dake fita daga jikin na miji wanda an tabbatar da cewa akan samu miniyyin da yewansu yakai millions wanda suke fita a lokacinda na miji yayi inzali amma saidai kwaya daya ne tak ke nasaran isowa cikin Overies wato inda ita kuma macen zata sako nata kwai wanda anan zasu hadu daga nan kuma sai su gangara zuwa mahaifa wanda hakan shine mafarin samun ciki.
Hanyoyin Samun Ciki Da Wuri
Ko akoi wasu dabaru da akeyi domin samun ciki da wuri sabanin yadda kowa ke sam, amsar itace eh akoi dabaru sosai na kimiyya wanda indai mutum ya daukesu yayi aiki dasu insha Allah za a dace cikin kankanin lokaci wanda a wannan gabar zanyi bayanin hanyoyin.
- Ki samu likita domin yayi miki duba izuwaga Vitamins masu kawo ciki da kuma isashen folic acid wanda wannan yanada tasiri sosai yana kare duk wani lahani dazai hana mace daukan juna biyu. folic acid wannan yana daga cikin babban abunda ya zama mataki na farko na daukan ciki ko reshin daukawa saboda haka yanada kyau ayi binciken wannan folic acid din.
- Sanin lokacin jinin haila wato wannan shima lokaci ne mafi dacewa da a rikayin jima’i saboda wannan lokaci ne da ake daukan ciki da wuri saboda haka ne ma yasa ya kamata mace tasan lokacinda take jinin haila. sannan akoi abubuwa da hanyoyi masu dama wanda mace zata auta ta gane lokacin da take Alada ko kuma lokacin tsayawar aladan nata wanda wannan zai taimaka sosai wurin samun ciki saboda haka ya kamata ace kafin ayiwa yarinya aure a nuna mata yadda zata kula da jinin ta.
- Zama kan gado bayan an gama jima’i shima wannan babban hanya ce dake taimakawa wojen samun ciki da wuri ana bukatar bayan miji da mace sun kammala jima’i anaso su bada ratar minti 15 zuwa 20 hakan domin miniyya ya karasa sauka zuwa mahaifa.
- Kada ka zama mai yewan yin jima’i, yewan yin jima’i bashine zaisa mace ta dauki ciki ba abunda ake bukata shine a rika samun tazara koda na kwana 1 saboda maniyyi yakan kai kwana 5 bayan fitansa daga jiki.
- Ma’aurata duka biyu anaso su rage damuwa ko wannensu ya rage damuwa da tunani saboda akan yakanyi tasiri sosai wurin samun juna biyu, saboda haka a lokacinda kuke jima’i domin samun juna biyu kuyi kokari ku cire damuwa a ranku domin shine yafi.
- Samun Lafiya anan ana bukatar daga kai har matarka ku kasance masu motsa jiki kada ku rika zama haka kawai babu motsa jiki.
Maganin Samun Ciki Da Wuri
Shin ko akoi magani da ake sha domin samun juna biyu, amsar itace eh akoi wanda wannan magani na baiwa Yayata kuma alhamdulillah an dace sosai wanda wannan magani ba wani abu mai tsada bane zan nuna muku yadda ake hadawa da yadda ake aiki dashi insha Allah.
Sannan kuma akoi maganin da za aiya aiki dashi na bature saboda ko kila karancin maniyyi shima yakan hana samun juna biyu saboda haka idan kasan cewa bakada karfin azzakari to lallai ina baka shawara ka rika shan maganin bature na karfin maza wanda hakan zai taimaka maka sosai wurin fitarda ruwan maniyyi.
Matsalar haifuwa bangaren mata
- Da farko za a samu karo/arabic gum
- Sai a nikashi kamar gari sai ta rika zuba chokali 2 a bakinta tana binshi da ruwa haka zatayi safe rana yamma.
- Sannan kuma ta tapasa karoo sai ta depo ruwan zafin ta rika shiga cikin ruwan dumin
- Sannan kafin ta kwanta barci ta jika karoon ta rika shafawa a alaurarta ta kwanta dashi insha Allah za a dace.
Matsalar haifuwa bangaren maza
- Za a samu Abarba/pineapple
- Sai a samu madaran saniya kindirmo ko sala duk wanda aka samu
- Sai a markada abarba a tabbata ya markadu
- Sannan a hadashi da madaran saniya a rika sha coffe daya safe yamma safe yamma